<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><title>Zaƃaƃƃe Na Allah, Shi LW111</title>
<lyrics>[V1]
 1) Zaƃaƃƃe na Allah, shi,
 Aikakke na ainihi,
 Nufin Allah duk ya yi,
 Ubangiji Almasihu.

[V2]
 2) Yesu aka kunyata,
 &quot;Shi ba wani abu ba,&quot;
 Aka ce. Ai, shi ya sa
 Aka raina Almasihu.

[V3]
 3) Shi, a jikin gungume,
 Ga shi nan kuwa, ɗaurarre!
 Aka kashe shi sosai,
 Mai alheri ne ya mutu.

[V4]
 4) Mutuncinsa aka ci,
 Zub da jini aka yi,
 Karƃar ceto aka ƙi.
 Jinin Yesu ya fanshe mu.

[V5]
 5) Riƙe shi ba dama fa,
 Ko a cikin mutuwa.
 Allah ma ya ɗaukaka
 Ɗansa, Yesu Almasihu.

[V6]
 6) In ya komo wata ran,
 Zai tashe mu daga nan,
 Har ya kai mu gun Uban,
 Rerawa ma yi wa Yesu</lyrics>
<hymn_number>111</hymn_number>
<author>Bliss, Philip Paul (1838-1876)</author>
</song>